4 Yuli 2025 - 20:40
Source: ABNA24
IRGC: Idan Har Wani Sabon Zalunci Ya Faru, Ba Za Mu San Wani Jan Layi Ba

Sardar Naeini, mai magana da yawun IRGC, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al-Mayadeen: Idan wani sabon keta iyaka ya faru kan Iran, martanin Iran zai kasance mai muni.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baity (As) -Abna- ya habarto cewa: ya qara da cewa saurin mayar da martanin da Iran ta yi ya wargaza lissafin makiya. Dole ne mu kalli manufofin yakin don sanin wanda ya yi nasara da wanda ya yi rashin nasara.

Makiya ba su cimma ko daya daga cikin manufofinsu ba a yakin karshe.

A wannan yakin, mun harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka sama da 2,000 a yankunan da aka mamaye.

Your Comment

You are replying to: .
captcha